IDAN KUNNE YAJI........
IDAN KUNNE YAJI........
Akwai wasu abubuwan da 'yan MATAN wannan zamanin suke yi, wanda ba qaramar illa yake musu ba, kuma yana daga cikin sanadin da yake jefasu cikin rudanin rayuwa da kaskancin yanayi..
Daga cikinsu akwai, kwadayi, da kaiwa kansu yanda bazasu iya zuwa a cikin irin yanayin da suke da yanda rayuwar yau ke gudana ba.
Asalima, sukan qudurta yin iyayoki wa samarinsu da kulla musu wata doka da bata da usuli.
Sukan bayyana wa samarimsu cewar sai kudi.... Sai mai gida iri kaza..... Sai mai mota iri kaza... Sai mai kyau iri kaza... Ba tare da sun tuna cewa komai na Allah ne... Kuma shine mai yin yanda yaso, shine mai cewa abu ya faru kuma sai aga ya farun, shine mai sanyewa mutum dukkan abinda yaso, ya hana mutum abin yake so.
Idan kince sai mai kudi, to kiyi la'kari da yaya mijin mamanki yake? Shima mai kudin ne? Idan mai kudin ne, to wayonshi ne ya bashi ko kuma ALLAH?
Idan kince sai mai gida iri kaza... To ke naku gidan yaya yake? Ki kuma tuna wayonku ne ya baku? Ko kuma ikon Allah ne?
Idan kince sai mai mota iri kaza... To menene ma'anar hakan? Motoci nawa ne a gidanku? Da kuke da motocin, wayonku ne ya baku ko kuma Arrahman ne yayi muku rahama kuka mallaka...?
Shin menene yasa bazaku aura daga wadanda suke masu tsoron Allah ba?? Sai masu tarin dukiya....
Shin baka tunanin cewar haihawar MATA a zamanin yau din nan yayi kusan ninka yawan maza?? Hakan ba zaisa kiyi kishi da alfahari ba idan kin samu kinyi aure??
Shin bakya tunanin cewar dukiya ko makamanciyarta ko kuma kishiyarta duk daga ALLAH ne?
Zakiyi iya auran talaka daga baya Allah yayi mishi daukaka ya zamo mai dukiya?
Haka nan, zaki iya auran mai kuddi daga baya cikin ikon Allah, Allah ya talautashi? Yaya zakiyi???
Guduwa zakiyi ki barshi saboda ya talauce? Ko kuma kuka zakiyi mishi akan ya dawo da dukiyar da ta kubuce mishi??
Ina son in jawo hankalin 'yan uwa MATA da su daure su dage wajen neman wadanda zasu zamo musu haske a rayuwarsu da duniya da lahira, ki zaba wa kanki da 'ya'yanki miji/uba nagari wanda zai iya gudanar muku da dawainiyarku.... Tarin dukia da kwadayinta baza suyi miki amfanin komai ba a lokacin da aka ce kin bisu domin su rufa miki asiri..
Allah ya aurar mana daku Sisters ya baku mazaje nagari masu sonku da tausayinku...


Comments
Post a Comment